Tattaunawa kan tsarin bayar da bashi ga masu kananan sana'oi 30.000 a jihar Kebbi

An gudanar da taron tsara dabarun yadda za'a tafiyar da shirin bayar da bashin masana'antu ga masu kananan sana'oi yau a ofishin Mai taimaka wa Gwamnan jihar Kebbi ta fannen inganta rayuwar Matasa watau Youth Empowerment Usman Buhari a harabar KUDA da ke garin Birnin Kebbi.

Usman Buhari yayin da yake jawabi tare da bayyana irin yadda sabon tsarin tafiyar da shirin zai gudana ya shaida wa wakilai na masu kananan sana'oi cewa an sami yaddar Gwamnati domin a aiwatar da shirin.

Ya kara da cewa a can baya an bayar da bashi ga al'umma wacce daga bisani aka sami 'yar matsala wajen biyan bashin , lamari da ya sa yanzu aka samar da sabon tsari wanda zai inganta yadda za'a karba da kuma yadda za'a biya bashin.

A wannan sabon tsari , za'a bayar da N250.000 ne gaba daya, amma za'a fara da bayar da N50.000 wanda bayan Mako biyu da karbar kudin za'a fara biyan bashin da abin da ya sauwaka.Amma tasari na farko shine dole ne mai bukata ya kasance yana da sana'a da kuma wajen da yake sana'ar a zahiri.

Sai kuma kasancewa a sami asusun ajiya na Banki idan har ba'a da shi a baya, daga bisani lambar BVN zai yi tasiri matuka sai kasancewa mai bukata yana cikin wata kungiya na taimakon juna watau Co-operative.

Usman Buhari yace shirin zai kai ma'aikatan har gida gida domin tabbatar da cewa sakon ya kai ga jama'a da ake bukata. Ya kuma jaddada cewa wannan kudi da za'a bayar bashi ne ba wai kamar wasu basuka da aka bayar ba a baya wadda zamani ya shude ba tare da waiwayar biyan kudin ba. Ya ce wanna kam kudin Banki ne kuma wajibi ne ayi tanadin yadda za'a biya Banki kudaden su matukar lokacin biyan kudin ya yi.

Wannan shirin ya kunshi sana'oi kamar tuyar masa, kosai, kabu kabu, aikin walda, gyaran babur ko mota, sana'ar yin cake, snacks, gyaran talabijin , waya, rewire, kapinta, da dai sauran su.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Mai ba Gwamnan jihar Kebbi shawara kan yadda za'a tallafa wa Matasa Alh. Usman Buhari Ali Gwandu, da Mai ba Gwamna shawara kan harkar Matasa Alh. Nafi'u Magini , da mai ba Gwamna shawara kan harkar watsa labarai na zamani Aisha Kuta da Masani kan harkar wayar Salula da sadarwa na zamani kuma Mawallafi Isyaku Garba, da Fitacce akan harkar Gadaje da kujeru na zamani Alh. Umar Jibrin da sauran Fitattu akan sana'oi daban daban.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN