• Labaran yau

  November 03, 2017

  Saurayi ya kashe budurwa domin ta fasa yin soyayya da shi

  Jakar tamu ta Magori ta leka kasar Liberia inda ta dauko mana labarin wani mutum da ya kashe wata Mata a yanayi na rashin imani da tausayi.Lamarin ya faru a gundumar Biokolleh na kasar ta Liberia da misalin karfe 10:00 na safe ranar Talata.

  Bayanai sun nuna cewa ita wannan Matar ta gamu da ajalinta ne a hannun wannan Mutum mai tsananin kishi da rashin hakuri bayan ta shaida masa cewa ita fa bata kaunansa kuma bata son ta ci gaba da yin soyayya da shi.

  Daga jin haka sai gogan naka ya harzuka ya far wa matar da duka har izuwa yanayi da ya kai ga kashe matar.  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Saurayi ya kashe budurwa domin ta fasa yin soyayya da shi Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama