Saurayi 'dan shekara 29 ya yi wa tsohuwa 'yar shekara 85 fyade har ta suma

Wani matashi ya fada hannun 'yansanda a garin Ilesha na jihar Osun bayan ya taushe tsohuwa 'yar shekara 85 yayi mata fyade har ta suma.

Kwamishinan 'yansanda na jihar Mr. Fimihan Adeoye ya shaida haka yayin da ya gabatar da wanda ake zargin ga 'yan jarida.

Ya kara da cewa yaron ya je gidan tsohuwar ce inda ya nemi taimako a bashi guri domin ya kwana har zuwa safe.Da talatainin dare sai matashi ya je ya kwankwasa kofar tsohuwan inda ya bukaci ta bude kofar domin yana son ya gaya mata wani abu.

Bude kofar ke da wuya sai matashin ya kayar da tsohuwar kuma ya yi mata fyade har sau biyu lamarin da ya sa ta suma.

Kwamishinan ya kara da cewa tsohuwar ta farfado a wani Asibiti yayin da ake ci gaba da bincike.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Saurayi 'dan shekara 29 ya yi wa tsohuwa 'yar shekara 85 fyade har ta suma Saurayi 'dan shekara 29 ya yi wa tsohuwa 'yar shekara 85 fyade har ta suma Reviewed by on November 01, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.