November 21, 2017

Muna kokarin mu wajen kare rayukan jama'a - Gwamnatin Zamfara

Sama da mutum 50 ne aka kashe 'yan kwanakin baya a karamar hukumar Shinkafi wanda ake zargin cewa barayi ne suka aikata wannan aikin, hakan ya kara zafafa zaman zullumi da ake yi a fadin jihar ganin cewa matsalar kisan mai-uwa-da -wabi ya sake dawowa a wasu yankuna na jihar Zamfara.

Mai taimaka wa gwamnan jihar Zamfara kan sha’anin tsaro Ibrahim Dosara ya ce ba gaskiya ba ne kalaman da ake cewa gwamnatin jihar tana sakaci a kan al’amarin.

Ya ce matsalar tsaro al’amari ne da ya shafi yankuna daban-daban na cikin kasa, kuma gwamnatin jihar a nata bangaren tana iyakar bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan matsalar.

Wata kungiya mai karajin kare hakkin bil'adama ta yi barazana cewa za ta maka Gwamnatin Zamfara a Kotu bisa zatgin gazawar Gwamnati wajen kare rayukan al'ummar jihar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

0 comments:

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Item Reviewed: Muna kokarin mu wajen kare rayukan jama'a - Gwamnatin Zamfara Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama