Motar daukan yashi tipa ta kashe mutum 4 bayan ta kwace wa direba

Wata motar tipa ta daukan yashi ta kashe mutum 4 tare da raunata wasu mutane bayan motar ta kwace wa direba kuma ta nufo cikin jama'a a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo ranar Lahadi.

Babura biyar da keke napep daya ne suka salwanta sakamakon hatsarin.

Rahotanni sun nuna cewa wani 'dan acaba, wata mata, wani yaro da wani mutum mai shago suna daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sakamako hatsarin wanda ya auku a Mayankar Moniya da ke garin Ibadan.

Direban tipar ya ruga da gudu kuma ya bace a cikin jama'a bayan aukuwar lamarin.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Motar daukan yashi tipa ta kashe mutum 4 bayan ta kwace wa direba Motar daukan yashi tipa ta kashe mutum 4 bayan ta kwace wa direba Reviewed by on November 06, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.