matasa 3 sun rasa ransu bayan an harbesu har lahira yayin aikin sintiri (Hotuna)

An harbe wasu matasa guda uku har lahira tare da jikata wasu da misalin karfe 8:15 pm ranar Asabar a garin Luebe da ke jihar Rivers.

Wani Basaraken al'umman Luebe Chief Micah Saakara ya tabbatar da faruwar Lamarin ya kuma zargi jami'an SARS a Bori da harbin mai uwa da wabi akan Matasan da suke aikin sintiri a yankin bayan Matasan sun gano cewa wasu daga cikin jami'an SARS suna raka wata mota da take dauke da haramtacciyar man fetur zuwa Ndoki a karamar hukumar Oyigbo.

A nashi jawabi shugaban karamar hukumar Khana Chief Hon. Gbene Lekue Zini yayi Allah wadai da aukuwar lamarin ya kuma yi kira ga Kwamishinan 'yansanda na jihar ya kaddamar da bincike domin a zakulo wadanda suka aikata wannan aikin domin a hukunta su.Ya kuma yi kira ga jama'an Luebe da cewa su kai zuciya nesa.
 Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
matasa 3 sun rasa ransu bayan an harbesu har lahira yayin aikin sintiri (Hotuna) matasa 3 sun rasa ransu bayan an harbesu har lahira yayin aikin sintiri (Hotuna) Reviewed by on November 13, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.