Mai yiwuwa Buhari zai tsaya takara a 2019

Sakamakon wadansu kalamai da shugaba Muhammadu Buhari ya furta a yayin ziyarsa a Abidjan na kasar Cote d'Ivoire inda ya halarci taron hadaddiyar kungiyar kasashen turai da na hadaddiyar kungiyar kasashen Afrika (EU-AU) Summit.Buhari ya nuna cewa kasancewarsa tare da Gwamnoninsa zai iya sama masa kuri'u a nan gaba .

Shugaba  Buhari ya ce "Da farko dai ina mai baku hakari sakamakon jiran mu har na tsawon lokaci wannan ya faru ne saboda na dage akan cewa yana da kyau Gwamnoni su halarci wannan taron.
Shi ne dalilin da ya sa na zo da su saboda idan kuka hadu da sauran 'yan Najeriya za ku ce ai Najeriya ce gabadayan ta ta zo domin Gwamnonin ku sun zo tare da shugaban kasa kuma ina ganin wannan zai iya zama sanadin kara samun kuri'u a wajena. Na ji dadi kwarai da kuka halarci wannan taron " kuma gaba daya sai aka washe da dariya yayin da wasu ke tafi .

**************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN