Lale marhaban ga sabin NYSC a jihar Kebbi,liyafar cin abinci (Hotuna)

Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya wa sabin masu yi wa kasa hidima na NYSC da aka turo nan jihar Kebbi Liyafar cin abinci na lale marhaban a gidan Gwamnati da ke garin Birnin kebbi ranar Laraba.

Yayin cin abincin , Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu wanda Mataimakinsa Alhaji Samaila Yombe Dabai ya wakilta ya shaida wa masu yi wa kasa hidima cewa Gwamnatin jihar Kebbi za ta yi iya kokarinta domin ganin ta inganta rayuwarsu tare da bukatar su yi walwala kamar kowane dan Najeriya.

Haka zalika Yombe ya bukaci masu yi wa kasa hidima su bayar da tasu gudunmuwa domin ci gaban jihar Kebbi da Najeriya gaba daya.Ya kara da cewa Matasa sune ginshikin ci gaban kowace al'umma.


 Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Lale marhaban ga sabin NYSC a jihar Kebbi,liyafar cin abinci (Hotuna) Lale marhaban ga sabin NYSC a jihar Kebbi,liyafar cin abinci (Hotuna) Reviewed by on November 23, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.