Gwamnatin Katsina ta bayar da tallafin awaki ga 'yan Makarantar Sakandare

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayar da tallafin awaki ga 'dalibai mata 'yan Makarantar Sakandare a garin Dutsinma yayin da yake kaddamar da shirin bayar da tallafin a Makarantar Sakandare na Arabiyya.

Kwamishinan Ma'aikatar Ilimi na jihar Katsina Halimatu Idris ta ce wannan shirin an kaddamar da shi ne domin hakan zai sa yaran su kasance masu dogaro da kan su.

Mrs Halimatu wadda Profesa ce ta ce bayar da tallafin yana daga cikin shirye shiryen Gwamnatin jihar domin inganta rayuwar talakkawan jihar ta hanyar sama masu ayyukan yi ko tallafi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Gwamnatin Katsina ta bayar da tallafin awaki ga 'yan Makarantar Sakandare Gwamnatin Katsina ta bayar da tallafin awaki ga 'yan Makarantar Sakandare Reviewed by on November 15, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.