Don Allah ku biya bashin manoma da aka baku - Alh. Samaila Yombe

Daga Isyaku Garba |

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai wanda shi ne shugaban Kwamitin karbo  bashin da manoma suka karba daga babban Bankin Najeriya ta shirin Anchor Borrower ya roki manoma da suka  amfana  da zubin farko na bashin cewa su kammala biyan bashin bisa tanadin shirin.

Wani bayani da ya fito daga hannun babban Darakta mai kula da nazari da tsaretsare na Mataimakin Gwamnan (Director Research and Documentation) Alh. Aliyu Jajirma ya ce Mataimakin Gwamnan ya bayyana rashin jin dadin sa akan yadda jama'a suka yi biris da biyan bashin cikin lokaci.

Bayanin ya kara da cewa Yombe ya roki jama'a akan su daure domin su biya kudaden sanin cewa kudaden arosu ne aka yi daga babban Bankin Najeriya saboda haka ya bukaci Manoma cewa su yi wa Allah da Manzonsa su biya kudin domin kauce wa yin amfani da tsari na karshe watau matakin hukuma domin karbar kudin.

Alh. Samaila Yombe ya yaba wa Gwamna Atiku Baguda kan wadataccen nazari da kyakkyawan lissafi na tafiyar da shugabanci  da ya kai ga nassara wajen harkar noma da samar wa manoma da bashi domin inganta sana'arsu ta noma.

Ya kuma ce nan ba da dadewa ba Kwamitin karbar bashin zai fara aiki domin ganin an karbo kudaden da manoma suka karba kuma suka ki mayarwa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafin mu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN