'Diyar Yombe ta bar jihar Kebbi tare da godiya ga Gwamna Atiku Bagudu

Nura Bena Daga Gidan Gwamnati |

Gwamnatin jihar Kebbi ta kara jaddada kudirin ta na ci gaba da hadin gwuiwa da kwararrun likitocin Duniya domin ingata sha'anin kiyon lafiya ga alummar jihar nan. 

Mataimakin Gwamnan jiha Alh. Samaila Yombe Dabai ne ya bayyana hakan alokacin da yake gabatar da wata kwarya- kwaryar kyauta ga wasu likitoci da suka yo tattaki zuwa nan jihar Kebbi  a matsayin su na 'yan gida kuma masu kishin jiha domin su bada tasu gudunmawa a sha'anin kiyon lafiya da Gwamnatin ta dauki nauyin gudanarwa a fadin jiha. 

Daga cikin su kuwa akwai diyar Mai girma Mataimakin Gwamnan jiha Alh. Samaila Yombe Dabai Watau Dr. Zainab Samaila Yombe Dabai tare da abokiyata Dr. Maryam. 

Dr. Zainab Samaila  Yombe Dabai da Dr. Maryam sun gode wa Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu akan karamci da aka nuna masu , tare da bada tabbacin goyon bayan su a kowane lokaci bukatar hakan ta taso domin bada tasu gudunmawa na ciyar da jihar Kebbi gaba.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
'Diyar Yombe ta bar jihar Kebbi tare da godiya ga Gwamna Atiku Bagudu 'Diyar Yombe ta bar jihar Kebbi tare da godiya ga Gwamna Atiku Bagudu Reviewed by on November 02, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.