Budaddiyar wasika ga makiya na ,ni ba dan luwadi bane - Adam A. Zango

Fitaccen jarumin 'dan wasan Fim na Kannywood kuma Mawaki Adam A. Zango ya rubuta wata budaddiyar takarda ga wadanda ya kira Makiyansa. A cikin wasikar Zango ya yi tsokaci akan yadda wadanda ya kira Makiya suka bata masa suna da kokarin ganin sun wulakantar da mutuncinsa.


"Ni ba 'dan Luwadi bane, ko Maroki ko Matsafi.Bana zuwa wajen Malaman tsibbu, bana zuwa wajen wani 'dan Siyasa ko 'dan Kasuwa ko Basarake domin na yi maula.Na yi tawakkali da abin da Allah ya bani.Kuma duk abin da kuka gani a guri na zufa na ne."

 "Abin da kawai zaku yi domin ku hana ni ci gaba shi ne ku kashe ni, kuma baku isa ba domin rayuwa ta a hannun Allah take. Makiya na miye yasa kuke kirkiro karya a kaina, kuna bata suna da mutunci na, na sha gaban ku "

"Kun kira ni Arne, 'dan Luwadi, Mazinaci amma har gobe masoya na suna kauna ta kuma suna sayen Fina Finai da wakoki na. Miye nayi maku ? Duk wanda na taimaka masa domin ya ci gaba sai ya dawo yana neman ya ga bayana"Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Budaddiyar wasika ga makiya na ,ni ba dan luwadi bane - Adam A. Zango Budaddiyar wasika ga makiya na ,ni  ba dan luwadi bane - Adam A. Zango Reviewed by on November 15, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.