Ba gaskiya bane cewa EFCC tana bincike na - Sheikh Isah Pantami

Sheikh Isa Pantami wanda shine shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) ya musanta zance da wasu ke yi cewa hukumar EFCC tana bincikensa.

Wannan ya biyo bayan  wadansu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ruwaito Ministan Sadarwar kasar Adebayo Shittu yana cewa gwamnatin tarayya tana jiran sakamakon wani binciken da hukumar EFCC take wa shugabannin hukumar NITDA.

Sai dai Sheikh Pantami ya musanta hakan, "karya aka rubuta a kanmu kuma idan mun samu wadanda suka aikata hakan, to kotu za mu kaisu," in ji shi.
Ya ce hukumar EFCC ba ta taba bincikarsa ba ko wani ma'aikacinsa tun da ya kama aiki da hukumar NITDA.
"EFCC sanya mana albarka take game da kokarin da muke na kawo gyara a hukumar NITDA," kamar yadda ya ce.


Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Ba gaskiya bane cewa EFCC tana bincike na - Sheikh Isah Pantami Ba gaskiya bane cewa EFCC tana bincike na - Sheikh Isah Pantami Reviewed by on November 07, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.