'Yansanda sun kama wadda ta yar da jariri da ta haifa a Yauri

Rundunar 'yansandan jihar Kebbi ta kama wata yarinya mai suna Gambo Suleiman bayan ta yar da jariri da ta haifa a kusa da gidan tsohon kantoman jihar Ekiti Col.Bawa .

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin Lahadi a garin Yauri kamar yadda ganau ba jiyauba ya shaida wa manema labarai.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Kebbi Mustapha Suleiman ya shaida aukuwar lamarin ,ya kara da cewa rundunar tana gudanar da bincike akan lamarin da ya nuna cewa Gambo bata da aure kuma za ta gurfana a gaban Kotu da zarar rundunar ta kammala bincike.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Hoto: pulse.ng
'Yansanda sun kama wadda ta yar da jariri da ta haifa a Yauri 'Yansanda sun kama wadda ta yar da jariri da ta haifa a Yauri Reviewed by on October 30, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.