Yadda masu yi wa mata fyade a Chochi lokacin ibadar dare suka fada hannu

Rundunar 'yansanda a jihar Enugu ta damke wasu samari guda tara wadda ake zarginsu da taushe mata kuma su yi masu fyade a lokutan ibada na dare da ake kira night vigil a garin Akpasha na karamar hukumar Nnaku na arewa.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar  Ebere Amaraizu ya ce nassarar kama wadanda ake tuhumar ya faru ne bayan wani bayanin sirri da rundunar ta samu cewa matasan sukan je Chochi ne kamar masu bauta amma idan mata sun fito zuwa daji da ke kusa domin su yi fitsari sai matasan su afka masu su ja su zuwa cikin daji su yi masu fyade.Wadanda ake zargin suna taimaka wa 'yansanda wajen gudanar da bincike.

 Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yadda masu yi wa mata fyade a Chochi lokacin ibadar dare suka fada hannu Yadda masu yi wa mata fyade a Chochi lokacin ibadar dare suka fada hannu Reviewed by on October 05, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.