Wata daya bayan bacewar daliba yar jss2 an gano ta a dakin saurayinta


An gano wata yarinya wadda daliba ce a makarantar sakandare ta Agbara da ke jihar Ogun.Yariyar 'yar JSS2 mai suna Asmau Ajibade an bayar da shelar bacewarta kimanin wata daya da ta gabata bayan bata dawo daga makaranta ba .

Asmau tana zaune tare da iyayenta Alhaji Rauf Adetona da Alhaja Ajarat Adetona, a Area 8, Road 810, Block AM, Plot 18, OPIC rukunin gidaje na Agbara kan titin Lagos-Badagry.

Punch ta ruwaito cewa an gano Asmau ne a dakin wani saurayinta mai suna John wanda mai gadi ne a  unguwar Igbo Elerin a yankin  Agbara.An kama John tare da wani abokinsa mai gyaran takalma mai suna Moses wanda da hadin bakinsa ne suka boye Asmau a dakin Moses.

Tuni John da Moses suka fada hannun 'yansanda a jihar ta Ogun yayin da ake ci gaba da bincike.


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Wata daya bayan bacewar daliba yar jss2 an gano ta a dakin saurayinta Wata daya bayan bacewar daliba yar jss2 an gano ta a dakin saurayinta Reviewed by on October 14, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.