Mata ta kwara wa miji tafasasshen ruwan zafin barkono a al'aura

Ngozi Obasi wata matar aure ce 'yar shekara 31da ta gurfana a gaban wani Kotun Majistare a Ebute Meta na garin Lagos bayan an zarge ta da kwara wa mijinta tafasasshen ruwan zafin barkono a al'auranshi bayan zafafan kalamai sakamakon takaddama da ta taso a tsakaninsu ranar Laraba.

An tuhumi Ngozi da yunkurin kisan kai wadda mai gabatar da kara na 'yansanda ya gabatar a gaban Kotu,amma Ngozi ta musanta hakan.

Alkalin Kotun ya dage shari'ar zuwa ranar 16 ga watan October domin ci gaba da sauraron shari'ar, daga bisani aka bayar da belin wadda ake tuhuma a kan N100.000.


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Mata ta kwara wa miji tafasasshen ruwan zafin barkono a al'aura Mata ta kwara wa miji tafasasshen ruwan zafin barkono a al'aura Reviewed by on October 07, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.