Mai gadi 'dan shekara 57 yayi lalata da yara mata 'yan makaranta 54

A kasar Afirka ta kudu wani tsoho 'dan shekara 57 wanda mai gadi ne a wata makarantar firamare a Orlando ta gabas ya fada hannun hukumomi bisa zargin yin lalata da yara 'yan mata guda 54 .

Majiyar mu ta labarta mana cewa  mai gadin da aka sakaya sunansa yayi amfani da dama da ya samu na gadi a makarantar domin ya yi lalata da yaran kamar yadda wasu yara 'yan aji 2 da aji 6  suka shaida wa shugaban Makarantar.

Wannan yasa shugaban Makarantar ta bukaci Malaman yaran su bincike su a cikin ajinsu,lamarin da ya haifar da sakamakon da ya nuna cewa tsoho mai gadi ya dade yana lalata da yara 'yan mata a Makarantar wanda adadinsu ya kai 54.

Ana kyautata zaton wannan tsoho zai gurfana a gaban Kotu a Pretoria bisa tuhumarsa da lalata da kananan yara.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Mai gadi 'dan shekara 57 yayi lalata da yara mata 'yan makaranta 54 Mai gadi 'dan shekara 57 yayi lalata da yara mata 'yan makaranta 54 Reviewed by on October 12, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.