Madugun sayar da mugan makamai ga 'yan fashi ya fada hannu

Zebulus Chiekezie wani tsoho ne mai shekara 64 'dan asalin garin Umukegwu -Akokwa a karamar hukumar Ideato na jihar Imo wanda 'yan sanda suka kama shi sakamakon kasancewarsa babban madugu kuma dillalin mugan makamai wanda ke sayarwa batagari makamai da albarusai.

Wannan tsohon ya fada hannun 'yansanda ne ta hannun sashen kwararrun 'yansanda da ke kula da harkar fashi da makami sashe tarayya.

An sami albarushi catridge 61 da bindigogi 4 wadanda basu da takardarizinin amfani da su a gidansa yayin gudanar da bincike.


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Madugun sayar da mugan makamai ga 'yan fashi ya fada hannu Madugun sayar da mugan makamai ga 'yan fashi ya fada hannu Reviewed by on October 13, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.