Kalli zaratan matan da suka yaki ISIS a Raqqa (Hotuna)

Wasu zaratan mayaka mata Kurdawa sun gudanar da shagulgula a garin Raqqa bayan an yi nassarar kakkabe mayakan ISIS wadda ta takura rayuwar mazauna garin har kusan tsawon shekara hudu.

Matan sunce sun shiga yaki da mayakan ISIS din ne domin su 'yantar da mata da yara da ISIS take bautar da su ta hanyar cin zarafi da sunan addini.

ISIS ta mulki yankin Raqqa da tsari na gallazawa da tozarci ga mata da lamarin baya misaltuwa a kasar Syria.

Haka zalika ISIS ta dinga kama yara mata tana sayar da su a matsayin karuwai ko bayi musamman 'yan tsirarrun kabilar Kurdish-Yazidi wadda  ake safaransu daga Raqqa.
Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Kalli zaratan matan da suka yaki ISIS a Raqqa (Hotuna) Kalli zaratan matan da suka yaki ISIS a Raqqa (Hotuna) Reviewed by on October 21, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.