Kalli motoci da mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ya kera (Hotuna)

Ko ka san cewa Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai mutum ne haziki mai baiwar gaske kuma ma'abuci kere kere kamar kowane hazikin mutum ?. Bayan kasancewa tsohon hazikin soja kuma kwararre wajen tukin jirgin sama wadda akasarin lamurransa na koyo da tukin jirgin sama yayisu ne a kasar Amurka Yombe shine ya kera wasu motoci yayin da ya sake fasalin wasu.

Wannan namijin hazakar Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ba kasafai akan sami shugaba da ke sadaukar da lokacinsa domin yin amfani da shi akan wani abin da zai amfani lokaci na kimiyya ko fasaha ba kamar yadda ya shafi rayuwar ci gaban zamani na bil'adama a yanzu.

Haka yake a Gwamnatance a jihar Kebbi karkashin shugabancin Gwamna Atiku Bagudu wadda ya bayar da muhimmanci akan harkar Fasaha da kere-kere da ka iya kaiwa ga amfani ga jama'ar jihar Kebbi.

Amma kalli irin motoci da Yombe ya kera kuma duka a nan cikin jihar Kebbi ya hada su.


 Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Kalli motoci da mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ya kera (Hotuna) Kalli motoci da mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ya kera (Hotuna) Reviewed by on October 22, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.