Hotuna: Yadda 'yan mata suka sha bulala domin a fitar masu da aljanu

Kimanin mata 2000 ne suka shiga layi domin a yi musu bulala wadda Malaman addinin Hindu ke aiwatarwa a Mujami'ar Achappan a Trichy na kudancin kasar India.

A kowane shekara akan kawo 'yan mata daga sassa daban daban domin su fuskanci irin wannan bulala da ya ke da asali da gargajiyar addinin Hindu.

Mafi yawan lokaci uwaye ne su da kansu ke kawo 'ya'yansu mata su shiga layi domin su jira yada za'a yi masu wannan bulala wadda akasari yakan kai awa biyar kafin layi ya iso kansu.

Wata yarinya da ta sha wannan bulala mai suna Vishakha ta ce ita iyayenta ne suka kawo ta saboda gashin al'auranta bai fito ba kuma jinin haila baya zuwa kamar yadda ya kamata a tsarin mata.

Wasu Mata tsofaffi sun goyi bayan wani Limamin Mujami'ar wadda yace yin bulala ga 'yan matan wani imani ne a addininsu cewa yakan kawar da shedanu da aljanu daga jikin 'yan matan ya kara da cewa al'ada ce da suka gada kaka da kakanni kuma ba zasu daina ba.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Hotuna: Yadda 'yan mata suka sha bulala domin a fitar masu da aljanu Hotuna: Yadda 'yan mata suka sha bulala domin a fitar masu da aljanu Reviewed by on October 08, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.