Gwamna Bagudu ya rantsar da Asabe Karatu a matsayin mukaddashin babban Joji na jiha

Isyaku Garba - Daga Gidan Gwamnati |

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya rantsar da Justice Elizabeth Asabe Karatu a matsayin mukaddashin Babban Joji  na jhar Kebbi a dakin taro na gidan Gwamnati yau Litinin 30 ga Oktoba 2017 .

Taron ya sami halartar Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai,Sakataren Gwamnatin jiha Babale Umar ,manyan Joji daga jihar Zamfara da kuma nan jihar Kebbi. Haka zalika Manyan Khadi da saran Lauyoyin Gwamnati da masu zaman kansu da sauran Kwamishinoni, da manyan jami'an Gwamnatati.

Gwamna Akiku Bagudu ya yaba wa bangaren sharai'a na jihar Kebbi musamman Manyan Joji bisa kyawawan halaye,mutunci,dattaku da sanin ya kamata.

Justice Elizabeth Asabe Karatu wadda asali daga yankin Masarautar Zuru ce a kudancin jihar Kebbi ta kasance mace ta farko a tarihin jhar Kebbi da ta rike mukamin babban Joji na jiha (Cheif Judge).

Haka zalika Gwamna Atiku Bagudu ya gode wa Sarakuna bisa namijin kokari da suke yi domin hada kan al'umma da aiki tukuru wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin jiha.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN