Gwamna Atiku Bagudu rahama ne ga jihar Kebbi - Mataimakin Gwamna Samaila Yombe

Daga Isyaku Garba - Birnin kebbi |

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai ya baiyyana Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu a zaman kyautan Allah ga jihar Kebbi bisa la'akari da hazaka,da aiki tukuru da yake yi ga al'umman jihar Kebbi.

Mataimakin Gwamnan ya ce abu ne da yake zahiri irin ci gaba da aka samu akan ababen da suka taba rayuwar jama'ar jihar Kebbi na ci gaba ta bangarori da dama idan an kwatanta yadda Gwamnatin Atiku ta same su da kuma irin ci gaba da ya bayyana a yanzu.

Yombe ya kara da cewa wadannan nassarorin sun kunshi gagarumin kokari da Gwamna Atiku Bagudu yayi wajen tafiyar da nazartaccen tsari wajen tafiyar da harkar kiwon lafiya ta hanyar samar da kayakin aiki ga dakunan gwaje-gwaje a Asibitoci tare da inganta matsayin Asibitoci a fadin jihar Kebbi.

Haka zalika Yombe yace bangaren hanyoyi kuwa a zahiri yake irin na mijin kokari da Gwamna Atiku ke yi wajen yin hanyoyi a fadin jihar Kebbi kamar yadda kowane 'dan jihar Kebbi zai shaida a Masarautar sa.

"Uwa uba harkar noma ba'a bar jihar Kebbi a baya ba yayin da Kebbi ta zama abin gwaji da misali ga kowace jihar da take son ta rungumi shirin noma a fadin Najeriya. Kamar yadda kuka gani Gwamna Atiku Bagudu bisa kyakkyawan nazari da iya tsara dabarun shirin harkar noma da gudanar da shugabanci ba tare da nuna ra'ayi ko banbanci ba yasa aka kai ga nassarori da aka samu a harkar noma a fadin jihar Kebbi"

"Salon shugabancin Gwamna Atiku Bagudu salon shugabanci ne da ke tafiya da nazari, fahimta da adalci da ke bukatar jama'a su fahimci haka wanda ta haka ne amfanin tsarin zai kai ga kowane 'dan jihar Kebbi sannu a hankali.Bisa wannan tsari Gwamnatin Aiku Bagudu za ta samar da ababen ingantawa tare da jin dadin rayuwar talakan jihar Kebbi ta hanyar shirye shirye da ta tsara wadda ake aiwatarwa sannu a hankali.

Mataimakin Gwamnan ya ce Gwamnatin Atiku Bagudu zata ci gaba da shirinta na inganta rayuwar Matasa a fadin jihar Kebbi ta hanyar koya masu sana'oi tare da bayar da tallafi wadda tuni tsarin tuntuba ya kankama akan shirin. Haka zalika Yombe ya ce hazikan Matasa ma ba'a bar su a baya ba sakamakon muhimmanci da Gwamna Atiku Bagudu ya bayar akan harkar kirkire-kirkire tare da son Matasa su sami wadatar dogaro da kansu.

"Yanzu haka Mai girma Gwamna Atiku Bagudu ya dukufa ne wajen ganin ya cika alkawarin da yayi wa jama'ar jihar Kebbi kuma tuni aka kammala cika galibin alkawurran"

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN