'Dan sanda ya bindige 'dan makaranta SS3 har lahira

Wani 'dansanda mai suna Corporal David Napoleon a jihar Bayelsa ya bindige wani yaro Tomizibe Johnson mai shekara 13 'dan aji SS3 na Makarantar sakandare har lahira sakamakon zafafar muhawwara da ta taso tsakaninsa da wasu matasa yayin da shi wanda aka bindige yake tsaye a wajen.

Rahotanni da ke karo da juna sun nuna cewa 'dansandan yana kare kanshi ne daga wani farmaki da matasa da wasu 'yan kungiyar asiri suka kai masa yayin da wasu bayanai ke nuna akasin haka a lamari da ya faru ranar Alhamis da dare.

Hukumar 'yansanda ta jihar Bayelsa ta kama tare da tsare 'dan sandan yayin da take gudanar da bincike akan lamarin.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
'Dan sanda ya bindige 'dan makaranta SS3 har lahira 'Dan sanda ya bindige 'dan makaranta SS3 har lahira Reviewed by on October 29, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.