'Dan dambe Ali kanin Bello zai dambace yau a Makera bayan hatsarin mota (Hotuna)

Fitaccen 'dan wasan dambe Ali kanin Bello wadda ya sami hatsarin mota 'yan kwanaki da suka gabata ya fita lafiya kalau kuma zai dambace a yau Alhamis tare da wasu manyan 'yan wasa kamar su Shagon Asharuwa ,Bahago Sani Guru mada,Ali Shagon Tuwo da Babawo.

Za'a gudanar da wasan damben a gidan wasan damben gargajiya da ke garin Makera. Bayanai sun nuna cewa Ali Kanin Bello bai sami halartar wasan damben a 'yan kwanakin baya bane sakamakon hatsarin da ya rutsa da shi inda wata yarinya ta gitta wa motarsa lamarin da ya haifar da hatsarin .

Yanzu haka komai ya kankama akan shirin wasan na dambe a garin Makera.


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
'Dan dambe Ali kanin Bello zai dambace yau a Makera bayan hatsarin mota (Hotuna) 'Dan dambe Ali kanin Bello zai dambace yau a Makera bayan hatsarin mota (Hotuna) Reviewed by on October 26, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.