B-kebbi: Matasa 10 sun gurfana gaban Kotu bisa zargin tayar da hankalin jama'a a garin Zauro

An gurfanar da wasu matasa goma 'yan asalin garin Zauro a gaban Alkali Mu'awiyya Shehu na Kotun Sharia ta 1 a garin Birnin kebbi bisa zargin hada baki domin a aikata laifi ,tayar da hankalin jama'a da hana ma'aikaci gudanar da aikinsa.

Mai gabatar da kara Kofur Faruku Muhammed ya gabatar da shaidu hudu a gaban Alkali a sharia mai lamba CR/171/2017 wadda ake tuhuman matasan guda goma wadanda suka hada da Kasimu Umar,Tukur Umar,Abubakar Umar,Badamasi Abubakar,Maniru Bello.

Sauran sun hada da Umar Riskuwa,Sufiyanu Mansur,Marwanu Shehu,Anas Umar,Badamasi Usman, da Abdullahi Shehu.

Bayanai sun nuna cewa takaddamar ta taso ne bayan matasan sun rubuta wata takarda zuwa ga uban kasar Zauro inda suka nuna rashin amincewarsu da kwamiti da aka kafa wadda za ta sa ido akan harkar luwadi,zinace-zinace,fyade,shaye-shaye da sace-sace.

Ana zargin matasan akan cewa ranar 13 ga watan Satumba,matasan sun je gidan uban kasar Zauro yayin da yake gudanar da taro na kwamiti tare da wakilan Malamai,Limamai,Dattijai da sauran manyan Mutanen kasar Zauro da misalin karfe 8:30 na dare.Kwatsam sai samarin suka fara jifar gidan da duwatsu da kwalabe lamarin da ya sa 'yansanda da ke gudanar da tsaro suka fito domin su fuskanci matasan.

Daga bisani matasan sun fasa gilasan motar daya daga cikin 'yansanda kana suka kai hari akan caji ofis na 'yan sanda a garin na Zauro.A bisa wannan dalili aka gabatar da matasa biyu da aka fara kamowa sakamakon shaida su da aka yi lamarin da ya sa su kuma suka taimaka wa 'yansanda domin zakulo sauran abokan nasu wajen aikata laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Da muka tuntubi wakilin wadanda ake zargin Barrister Ahmadu Zumaru ya bayyana mana cewa shari'a sabanin hankali ne,kuma bai dace wasu mutane su yi amfani da matsayin su domin su dora wa mutane dokoki da babu adalci a ciki ba,ya kara da cewa ya kamata a bi ka'idar doka da tsarin mulki wajen kirkiro dokoki da za'a dora wa al'umma.Ya kuma nuna gamsuwa akan yadda shari'ar ke tafiya kawo yanzu.

Shi kuma Alhaji Sani Zauro (Hukuma) cewa yayi wannan kwamiti ya fi shekara takwas da aka kafa shi saboda haka su kam sun bi ka'idar doka kafin su kafa waannan kwamitin.Ya kara da cewa su a shirye suke domin su gan cewa tabbas sun kare mutunci da martabar kasar Zauro dangane da lamarin tarbiyyan al'umma ya kuma kara da cewa ba gudu ba ja da baya kuma sun shirya tsaf domin tunkarar wannan lamari a duk inda lamarin zai kai.

Alkali Mu'awiyya ya dage shari'ar zuwa Talata 10 ga watan Oktoba domin ci gaba da shari'a yayin da aka bayar da belin wadanda ake tuhumar.

Isyaku Garba daga Birnin kebbi.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN