B-kebbi: Jami'in NSCDC ya kashe kan shi ta hanyar rataya a Badariya

 18.Oct.2017  Isyaku Garba - Birnin kebbi

Mazauna unguwar Badariya a garin Birnin kebbi sun wayi gari cikin mamaki bayan labari ya bazu wadda ke zargin cewa wani jami'in NSCDC mai suna Reuben ya rataye kanshi a gidansa har ya mutu da misalin karfe 9:00 na dare ranar Talata.

Bayanai sun nuna cewa marigayin yayi ta zirga-zirga zuwa Asibiti akan lamarin rashin lafiyar iyalinsa kimanin makonni biyu da suka gabata.

Wata majiya ta shaida mana cewa hatta yammacin jiya Talata Reuben yana tare da sauran jami'an NSCDC a gurin da yake aiki a ofishinsu na kusa da randabawul na Asibitin Sir Yahaya amma babu wata alama da ta bayyana da zai nuna cewa ko yana cikin wata damuwa.

Bincike ya nuna cewa an adana gawar Reuben a dakin ajiye gawa na Asibitin Sir Yahaya yayin da hukumomin NSCDC  ke gudanar da bincike akan musabbabin faruwar lamarin.

Reuben wanda 'dan tsohon Soja ne da yayi aiki da Bataliya ta 81 a garin Birnin kebbi,ya bar mahaifiyarsa da 'yaya biyar daga cikinsu babbar diyarsa ta kammala Makarantar sakandare  kuma ta lashe takardun sakamakon jarabawa gaba daya.

Yunkurin mu na mu ji ta bakin mai magana da yawun hukumar NSCDC ta jihar Kebbi game da lamarin ya ci tura saboda lambar wayarsa ta salula bata shiga kafin mu rubuta wannan labarin.Amma kakakin hukumar 'yansanda na jihar Kebbi Mustapha Suleiman ya tabbatar mana da faruwar lamarin inda ya shaida mana cewa hukumomi na gudanar da bincike akan lamarin

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
B-kebbi: Jami'in NSCDC ya kashe kan shi ta hanyar rataya a Badariya B-kebbi: Jami'in NSCDC ya kashe kan shi ta hanyar rataya a Badariya Reviewed by on October 18, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.