B-kebbi: Bikin ranar samun 'yancin Najeriya a jihar Kebbi (Hotuna)

Da safiyar yau a babban filin wasa na sakatariyar Haliru Abdu da ke cikin garin Birnin kebbi an gudanar da bikin murnar cikan Najeriya shekara 57 da samun 'yanci daga kasar Britaniya watau England ranar 1 ga watan Octoba 1960.

Bikin na yau ya sami halartar fitattu daga cikin manyan jami'an Gwamnati,'yan Majalisar Dokoki na jihar Kebbi,Manya da kananan 'yan kasuwa,Ma'aikatan Gwamnati,kungiyoyi masu zaman kansu da sauran jama'a har da yara 'yan Makarantun firamare da sakandare.

Jami'an tsaro na 'yansanda,Civil Defence,Immigration,Prisons Service ,Vigilante da 'yan Makaranta sun kayatar da masu kallo da pareti wadda sashen kadekade na rundunar 'yansanda suka aiwatar.

Gwamna Atiku Bagudu ya roki jama'ar jihar Kebbi su yi wa jihar Kebbi da Najeriya addu'a domin samun nassara  da zaman lafiya.Gwamnan ya ci gaba da bayani cewa Gwamnatinsa tare da hadin guiwa da gwamnatin tarayya suna kokartawa domin ganin an kammala aikin hanyar Yauri zuwa Jega cikin lokaci.

Ya kuma yi bayani akan nassarori da Gwamnatinsa ta samu wajen gudanar da hanyoyi a Masarautu 4 da ake da su a jihar Kebbi wadda ya ce babban alhairi ne daga karshe ya kuma gode wa Sarakuna guda 4 da ake da su a jihar Kebbi tare da gabadayan jama'ar jihar Kebbi.Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
B-kebbi: Bikin ranar samun 'yancin Najeriya a jihar Kebbi (Hotuna) B-kebbi: Bikin ranar samun 'yancin Najeriya a jihar Kebbi (Hotuna) Reviewed by on October 01, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.