Asirin matashi ya tonu bayan yayi kokarin saka tabar wiwi a motar wani

Asirin wani matashi ya tonu bayan yayi kokarin saka wasu manyan kunshi guda biyu cike da tabar iblis ko wiwi a titin Elelenwo da ke garin Portharcourt na jihar Rivers.

Mai motar Victor Odili yace ya tsaya ne a gurinda ya ajiye motarsa domin ya yi zance da wani abokinsa haka kawai sai ya hango wannan mutumin yana cuku cuku a motarsa.

Bayan ya auna hankalinsa sai ya gan cewa ashe wiwi ne matashin ya saka masa a mota.

Idan baku manta ba,'yan kwanakin baya wani Pasto a garin na Portharcourt ya gano wata babban laida cike da tabar wiwi da aka sanya a motarsa.Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Hoto:nationalhelm 
Asirin matashi ya tonu bayan yayi kokarin saka tabar wiwi a motar wani Asirin matashi ya tonu bayan yayi kokarin saka tabar wiwi a motar wani Reviewed by on October 10, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.