An rufe Asibiti bayan an sami wani Nurse yana tiyata

Hukumomi a jihar Oyo sun rufe wani Asibiti mai zaman kansa bayan jami'an da ke sa ido na sashen kula da ayyukan Asibitoci masu zaman kansu sun kama wani Nurse yana aikin fida (Theatre) akan wani mara lafiya a Asibitinsa.

Wanda aka kama shine mai Asibitin  Agbejemate Hospital and Maternity Centre wanda ke unguwar Iseyin. An same shi yana gudanar da aikin fida akan cutar gwaiwar ciki ko hernia.

Majiyar mu ta shaida mana cewa mai Asibitin tsohon Nurse ne da ya dade a bangaren fida a Asibitin gwamnati kafin yayi ritaya ya bude nashi Asibitin.

Hukumomi sun bukaci ya gabatar da kanshi a ma'aikatar lafiya ta jihar Oyo bayan an rufe wasu karin Asibitoci guda biyar bisa zargin rashin kwararrun ma'aikatan jinya ko Likitoci, da rashin ingantattun kayan aiki ko kazanta .

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN