An kama Matar da ta sayar da diyarta akan N280.000

A ranar Talata da ta gabata aka kama wata mata mai suna Olubunmi Funke inda ake zargin ta da sayar da 'diyarta ga wata mata mai suna Abibat Oyesanya akan Naira 280.000 a jihar Ogun.

Majiyarmu ta shaida mana cewa Abibat Oyesanya tana cikin masu safaran yara kanana a wannan yankin.

Olubunmi Funke ta ce bayan Mijinta ya rabu da ita hatta karuwanci ma ta yi domin ta hada kudaden da zata biya bashin da ake bin ta amma abin ya faskara shi ya sa ta sayar da diyarta.

Ta yi wannan bayani ne ga Manema labarai a Elaweran Hedikwatar 'yansanda na jihar Ogun yayin da aka gabatar da ita da sauran masu laifi ga Manema labarai.

Haka zalika 'yansanda sun kama Abibat Oyesanya da Morenike Shittu bisa zargin  dillancin yara a fadin jihar.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
An kama Matar da ta sayar da diyarta akan N280.000 An kama Matar da ta sayar da diyarta akan N280.000 Reviewed by on October 26, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.