An kama korarren 'dansanda da ya zama 'dan fashi

Wani korarren 'dansanda  Kenneth Chikwe ya fada hannun hukumar 'yansanda na jihar Anambra bayan shi da abokin sa sun kwace motoci a hannun wasu 'yanuwan juna a garin Akwa.

Kwamishinan 'yansanda na jihar ne Mr.Garba Umar ya shaida wa manema labarai haka a ofishin 'yansanda na Amawbia da ke karamar hukumar Awka ta yamma a jihar Anambra.

Kwamishinan yace an kama korarren 'dansandan da raunukan albarushi a jikinsa wadda bayaninsa ya kai ga kamo Uzohu Livingstonedan shekara 51 a garin Owerr na jihar Imo.

An sami kwato mota kirar  Range Rover, Toyota Hilux, bindiga kirar AK-47 da albarusai 20,bindiga kirar K-2 da albarushi 15 da karamar bindiga Pistol kirar gida da bindiga mai barin wuta guda daya.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

No comments:

Rubuta ra ayin ka