An kama 'dan sandan da ya yi wa matashi kazafin kasancewa kwarto

Idan baku manta ba kwanakin baya mun kawo maku labarin wani saje na 'yansanda wanda ya shirya mugunta inda yayi wa wani matashi Ese Idehen kazafi cewa ya yi kwartanci da matarshi lamarin da ya kai ga cin zarafin wanda ake zargin a garin Benin na jihar Edo.

Wani sabon labari ya nuna cewa bayan gabatar da takardar koke daga Lauyan wanda aka ci zarafi ga Kwamishinan 'yansanda na jihar ta Edo,an kama saje Nagbama Osakpamwan Eboigbe kuma yanzu haka yana fuskantar tuhuma kamar kowane mai laifi.

Bayanai sun nuna cewa hatta 'yansanda da suka taimaka masa domin a kulle wanda ake zargin a cikin caji ofis su ma suna fuskantar shari'a na cikin gida bisa tsarin hukumar 'yansanda.Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
An kama 'dan sandan da ya yi wa matashi kazafin kasancewa kwarto An kama 'dan sandan da ya yi wa matashi kazafin kasancewa kwarto Reviewed by on October 18, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

SANARWA

Seniora Tech tana sanar da jama'a cewa ta koma TAUSHI PLAZA shago mai lamba 50 a hawa na sama yamma da gidan Wazirin Gwandu. Ahmadu Belloy way,Birnin kebbi, jihar Kebbi.
Tuntube mu domin Flashing, cire security na waya ko neman sani game da yanar gizo da sauransu.
Ko ka kira 08087645001
Powered by Blogger.