Yaro 'dan shekara 16 mai sayar da mugan makamai ya fada hannu

Wani yaro mai suna Onyedikachi Iyaka dan karamar hukumar Ehime Mbano ya fada hannun yansanda jiya a jihar Imo bayan an kamashi yana sayar da mugan makamai tare da wasu kayakin aiki na ma'aikata.

Daga cikin kayakin da aka kamashi da su sun hada da albarushi 400 na bimdigar GPMG, albarushi1,016 na bindiga kirar AK47, bindigar AK 47 guda daya , rigar kare albarushi na soja guda daya, na 'yan sanda guda daya, rigar ruwa na 'yansanda guda daya, da jar hula guda daya.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Imo Chris Ezike ya yi mamakin ganin wadannan kayaki wadda yace makamin zai iya kakkabo jirgi mai saukan ungulu.

Yayin da yake zantawa da manema labarai Onyedikachi ya shaida masu cewa kayakin na yayanshi ne mai suna Jeff Iyaka wandda ya ranta na kare a halin yanzu, ya kuma ce yayan nashi yana sayar da kwalin albarushi akan N7000..

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Yaro 'dan shekara 16 mai sayar da mugan makamai ya fada hannu Yaro 'dan shekara 16 mai sayar da mugan makamai ya fada hannu Reviewed by on September 12, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.