Uwa da 'yayanta 5 sun mutu bayan sun sha fate mai guba a Zamfara

Wani ibtila'i ya faru a Shiyar Ajiya a karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara inda wata mata da yara biyar har da makwabcinta daya suka mutu sakamakon wani fate da suka sha wadda ake kyautata zaton cewa yana dauke da guba.

Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara Prof.Abdullahi Shinkafi ya tabbatar da faruwar lamarin yayinda saura ke karbar magani a Asibiti kamar yadda Premium Times ta labarta.

Majiyarmu ta labarta mana cewa hukumomi a Zamfara sun tura tawagar kwararru domin gano musabbabin aukuwar wannan lamarin.

Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Uwa da 'yayanta 5 sun mutu bayan sun sha fate mai guba a Zamfara Uwa da 'yayanta 5 sun mutu bayan sun sha fate mai guba a Zamfara Reviewed by on September 04, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.