Soji sun kama dan fashi a jihar Zamfara

Dakarun rundunar soji ta 1 da ke gudanar da aikin operation sharan daji a Magami na karamar hukumar Gusau sun yi nassarar tarwatsa gungun wasu 'yan fashi da makami da suke gudanar da fashi akan hanyar Jangebe zuwa Gusau bayan an sanar da su abinda ke faruwa.

Sojin sun tunkari wajen da lamarin ke faruwa a daji kuma nan take suka yi artabu da yan fashin wadda daga bisani suka tsere da raunukan albarushi yayin da aka kama daya daga cikin su. Dakarun sun sami bindigar hannu kirar gida guda 1, wayar salula Tecno guda 1, jakar hannu na mata guda 1, lalita 1 da tsabar kudi N20.000.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Soji sun kama dan fashi a jihar Zamfara Soji sun kama dan fashi a jihar Zamfara Reviewed by on September 28, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.