• Labaran yau

  September 05, 2017

  Rundunar Sojin Najeriya ta fara tura tankokin yaki zuwa kudu maso gabas

  Rundunar Sojin Najeriya ta fara tura tankokin yaki da kayakin fada zuwa yankin kudu-maso-gabas,wannan ya biyo bayan karin dakarun yakin na Sojin kasa da aka kara yawansu a wannan yankin don shirin tunkarar kawane irin barazana gabanin zabe da za'a gudanar a yankin.

  Majiyar mu ta labarta mana cewa rundunar 'yan sanda itama tana jiran wani umarni daga Kotu a Abuja domin a kama makiyin zama lafiyannan Nnamdi Kanu bayan Gwamnatin tarayya ta shigar da kara inda take bukatar Kotu ta janye belin da ta ba Nnamdi Kanu.  A 'yan kwanakin baya ne rahotanni suka bayyana a shafukan yanar gizo wadda ke nuna irin kalami na cin mutunci ,rashin ragowa da neman fitina da Nnamdi Kanu ke ta yi.  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rundunar Sojin Najeriya ta fara tura tankokin yaki zuwa kudu maso gabas Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama