Pasto da yace Duniya za ta zo karshe ya canja ra'ayi

David Maede Pastor masani taurari da ya yi harsashen cewa Duniya zata zo karshe ranar 23 ga watan Satumba a mako da ya gabata ya canja ra'ayinsa.Maede ya ce duk da yake Duniya bata zo karshe ba a 23/9 amma ababe dayawa za su canja daga farkon watan Oktoba.

Maede ya ci gaba da cewa ba kamar yadda aka zata ba da farko cewa Duniyar "Planet Nibru" zata yi karo da Duniyar mu ta Earth a cikin Al'arshi wadda hakan zai kawo karshen Duniyarmu.

Ya kuma kara da cewa maimakon haka, tabbas daga Oktoba ilahirin ababe zasu canja ta yadda ba zasu sake komawa daidai ba a cikin rayukkan mutane da dama a Duniya musamman a makonnin farko farkon na watan Oktoba.

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Pasto da yace Duniya za ta zo karshe ya canja ra'ayi Pasto da yace Duniya za ta zo karshe ya canja ra'ayi Reviewed by on September 23, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.