• Labaran yau

  Mi yasa dangantaka ya yi tsami tsakanin Rahma Sadau da Ali Nuhu ?

  Dangantaka tsakanin fitattun 'yan wasan kwaikwayon Hausa na Kannywood Ali Nuhu da Rahma Sadau ya fara tsami sakamakon rashin sanya Rahma Sadau a wani Fim "Abota" da yanzu haka ake hadawa karkashin kulawar Ali Nuhu wadda ubangidanta ne a harkar wasannin Kannywood.

  Wannan shine musabbabin rashin jin dadi daga fitacciyar 'yar wasan wadda tuni ta kalubalanci Ali Nuhu akan wannan lamarin kamar yadda majiyar mu ta labarta mana.

  A bara ne kungiyar kula da da'ar 'yan wasa MOPPAN ta dakatar da Rahma Sadau daga taka rawa a Finafinai don ladabtarwa, amma Rahma ta fito a Finafinai da dama bayan hukuncin na MOPPAN.

  Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mi yasa dangantaka ya yi tsami tsakanin Rahma Sadau da Ali Nuhu ? Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama