Matasa 2 sun haukace bayan sun mayar da motar da suka sace

Wasu matasa guda biyu sun haukace bayan sun saci wata mota kirar Nissan Fuga daga wani wurin shakatawa na Bamburi  a Mombasa kuma yayin da suke tafiya da motar sai aljanu suka shigesu lamarinda ya sa suka tsayar da motar suka tube zindir sai kawai suka fara sheka  rawa kamar yadda Kehawatungu ta ruwaito.

Motar da suka sata na wani Anwarali ne a gundumar Kisauni. Bayanai sun nuna cewa barayin sun sato motar ce daga Bamburi Mtambo kan hanyarsu ta zuwa  Bamburi Mwisho sai wannan lamarin ya faru da su.

Matasan sun dinga diban wani ruwan cabo da ke kusa da su suna ta wanka kuma suna waka suna rawa,sun kuma kama wani maciji da ke wucewa ta kusa da su inda daya daga cikinsu ya rataya a wuyansa yayin da yake rawa kuma yana barazanar cewa zai jefa macijin a kan jama'a da suke kallon su.

Daga bisani 'yansanda sun tasa keyarsu zuwa caji ofis na garin Bamburi.


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Matasa 2 sun haukace bayan sun mayar da motar da suka sace Matasa 2 sun haukace bayan sun mayar da motar da suka sace Reviewed by on September 07, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.