Magidanci ya kashe diyar kishiyar matarshi mai shekara 3

Hukumar 'yansanda na jihar Katsina ta kama wani matashi Akilu Alh.Saidu bayan ya kashe diyar kishiyar matarshi  mai shekara uku da duka a garin 'Yan kara a karamar hukumar Faskari.

Akilu ya shaida wa 'yansanda yayin da suke gudanar da bincike cewa ya ja yarinyar ne har zuwa wani kangon gida daga bisani ya murde wayarta da karfin tsiya lamarin da ya haifar da mutuwar yarinyar.

Kakakin hukumar yansanda na jihar DSP Gambo Isah ya shaida wa manema labarai cewa Akilu ya amsa laifinsa ya kuma kara da cewa ya aikata laifin ne sakamakon kwayoyi da ya sha wadda ya juya masa tunani.

DSP Gambo yace rundunar 'yansanda zata gurfanar da Akilu a gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Magidanci ya kashe diyar kishiyar matarshi mai shekara 3 Magidanci ya kashe diyar kishiyar matarshi mai shekara 3 Reviewed by on September 26, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.