Kalli yadda motar wani Bahaushe ta take saurayi har lahira a Aba

Yanzu  haka akwai rudani da damuwa sakamakon mutuwar wani matashi bayan wata babban motar daukan kaya da rahotanni suka nuna cewa wani Bahaushe ne yake tukata ta takeshi lamarinda yayi sanadin mutuwarsa nan take a garin Aba na jihar Abia.

Bayanai sun nuna cewa ganin hakan ke da wuya sai Bauhaushen kuma direban motar ya ranta na kare saboda har yanzu da muka rubuta wannan labarin ba'a san inda yake ba .Wata majiya ta ruwaito  cewa direban ya gudu ne bayan ya gan mutane suna ta dafifi a wajenda lamarin ya faru.

An girka jami'an tsaro a  wajen da lamarin ya faru domin a kare yiwuwar karya doka da oda.
Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Hoto: Nationalhelm
Kalli yadda motar wani Bahaushe ta take saurayi har lahira a Aba Kalli yadda motar wani Bahaushe ta take saurayi har lahira a Aba Reviewed by on September 02, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.