• Labaran yau

  September 10, 2017

  Kalli yadda 'dan sanda ya wulakanta kansa bayan ya bugu da barasa

  Hotuna da bidiyo na wani 'dan sanda da ya kwankwadi barasa yayi makas ya bayyana a shafukan yanar gizo wadda ke nuna yadda 'dan sandan cikin kakinsa na aiki ya fadi kuma gogan naka ya share da barci a gefen ruwan cabo .

  Irin wannan abin kunya yakan faru lokaci zuwa lokaci a Najeriya musamman game da jami'an rundunar 'yan sanda.

  Shidai wannan hoton an sakaye sunan 'dan sandan da wurin da lamarin ya faru saboda dalilai na tsaro amma hoton ya fara bayyana ne a shafin PoliticsNGR.

  Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli yadda 'dan sanda ya wulakanta kansa bayan ya bugu da barasa Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama