Kalli yadda aka kashe wani jami'in tsaro a wajen aiki

Rahotanni da ke fitowa daga jihar Rivers sun nuna cewa an sami matsala tsakanin wasu jami'an 'yan sanda na bangaren SARS su biyu da suka kai samame a gida wani da ake zargi da aikata laifi,kuma yayin da suke a gidan sai mai laifin ya kira wani abokinsa da yake seshen musamman na safeto janar inda ya shaida masa cewa 'yan fashi sun zo gidansa.

Nationalhelm ta ruwaito cewa dataga isowarsu sun bukaci 'yan sanda na bangaren SARS su mika makamansu amma wani safeto ya ki bayan ya karanta masu lambarsa ta aikin 'dan sanda, ya bukaci su kira layin Kwamishinan 'yan sanda na jihar domin su tantance inda su kuma suka mayar da martani cewa su basa karabar umarni daga Kwamishina.

Shi kuma safeto dan SARS sai ya ki mika makaminsa lamarinda ya sa suka buda masa wuta kuma nan take ya mutu.

Bayanai  sun nuna cewa yanzu haka ana gudanar da bincike akan musabbabin aukuwar lamarin.
Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Kalli yadda aka kashe wani jami'in tsaro a wajen aiki Kalli yadda aka kashe wani jami'in tsaro a wajen aiki Reviewed by on September 13, 2017 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

ISYAKU TV

Powered by Blogger.