Jam'iyar APC ta bukaci Aisha Alhassan tayi murabus

Jam'iyar APC tayi kira ga Ministan harkokin Mata Aisha Alhassan da tayi murabus sakamakon abinda ta kira kalaman rashin mutunci da Ministan tayi akan shugaba Buhari a 'yan kwanakinnan tare da nuna goyon baya ga Atiku Abubakar.

Ministan wadda ake wa lakabi da Mama Taraba ta fuskaci kalubale daga kafofi da dama tun lokacin da tayi wata hira da BBC inda tayi wasu kalamai da bai yi wa wasu manyan 'yan jam'iyar APC dadi ba.

Yayin da yake amsa tambaya daga manema labarai a hedikwatar jam'iyar APC a Abuja, Inuwa Abdulkadir wadda jigo ne a kwamitin tafiyarwa kuma mataimakin chiyaman na gabas maso arewa na jam'yar ta kasa ya ce "Kalaman da Ministan ta furta kalamai ne na rashin mutunci kuma ya zama wajibi tayi murabus saboda lamarin ya zama cin amana" .

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Jam'iyar APC ta bukaci Aisha Alhassan tayi murabus Jam'iyar APC ta bukaci Aisha Alhassan tayi murabus Reviewed by on September 09, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.