September 17, 2017

Hotuna: 'Yan IPOB sun kone Masallaci a Ogrute jihar Enugu

Wasu da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne sun banka wuta a wani Masallaci da asubahin ranar Asabar a garin Ogrute hedikwatar karamar hukumar Igbo-Eze na Arewa a jihar Enugu, lamarin da ya sa Masallacin da kayakin da suke cikinsa suka kone kurmus.

Daily Post ta ruwaito cewa al'umma Musulmi a garin Ogrute suna cikin fargaba sakamakon wannan lamari inda suka yi kira ga Hukumomi su kawo masu dauki.

Wata majiya ta labarta cewa Gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ya bada Naira Miliyan daya domin a sake gina wani Masallaci.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Enugu SP Ebere Amaraizu ya tabbatar da faruwar lamarin.Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

0 comments:

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Item Reviewed: Hotuna: 'Yan IPOB sun kone Masallaci a Ogrute jihar Enugu Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
Koma Sama