Hotuna: 'Yan daban siyasa sun kai wa 'yan jarida hari a Kotu

Rahotanni daga Ilori na jihar Kwara sun nuna cewa wasu 'yan daban siyasa sun tayar da hargitsi da ya kaisu ga afka wa 'yan jarida da suka je wani babban Kotu domin sauraron shari'a tsakanin shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da mai gidan jaridar Sahara Reporters.

Saraki yayi karan Omoyele Sowere bisa zargin bata masa suna inda yake neman Kotu ta sa Omoyele ya biya shi Naira biliyan hudu.

Bayani sun nuna cewa daga isowar motar da ke dauke da 'yan jarida a bakin kofar shiga harabar Kotun sai matasan suka zaburo suka fara rigimar da ya kai ga fasa gilasan motar kafin 'yan sanda su shawo kan lamarin.

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Hotuna: 'Yan daban siyasa sun kai wa 'yan jarida hari a Kotu Hotuna: 'Yan daban siyasa sun kai wa 'yan jarida hari a Kotu Reviewed by on September 16, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.