• Labaran yau

  September 01, 2017

  Hotuna: Kotu ta daure barawon ragon Sallah wata 6 a gidan Yari

  Yayin da ake shagulgulan babban Sallah wani matashi dan shekara 30 Suleiman Awokunle zai share watanni 6 a gidan Yari bayan an kamashi da laifin satan ragon Sallah da wani Saka Idowu ya saye.

  Suleiman ya shiga gidan Idowu kwanaki kadan kafin Sallah da misalin karfe 6 na asuba inda ya arce da ragon a garin Ire daga bisani aka kamashi bayan an zagaya da shi a cikin gari sai aka mika shi ga hukuma lamarin da ya kaishi ga bayyana a gaban Alkalin wata Kotun Majistare.

  Daga bisani dai Kotu ta daure Sueiman wata shida a gidan Yari bayan ta same shi da laifin satan ragon Sallah.


  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotuna: Kotu ta daure barawon ragon Sallah wata 6 a gidan Yari Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama