• Labaran yau

  September 06, 2017

  Hayakin janareto yayi sanadin mutuwar maigida da matarsa

  Hayakin janareton wutan lantarki yayi sanadin mutuwar wani mutum da matarsa yayin da suka kwanta barci suka bar janareton yana aiki kusa da kofar dakinsu da dare,an sami gawar Omafidon Otitie da matarsa a mace cikin dakinsu ranar Litinin a karamar hukumar Okpoba-Okkha da ke cikin jihar Edo.

  Daya daga cikin yayan mamatan ya tsira inda yake karbar magani yanzu haka a Asibiti.  Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hayakin janareto yayi sanadin mutuwar maigida da matarsa Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama